Ca! Ca!!
Su na magana kaina
Yayin da na juya don na kallesu
Cikin kunya su ka juya su ka kalli wani gun
Ca! ca!!
Su na rada kaina
Yayin da kuma na kusancesu
Sai batun hirarsu ya canja
Ca! ca!!
Sauran ‘kiris nai tuntu’be na fadi
Domin idanuwan da su ka kuramin
Sun jefa min arwa
Kafata kuma ta harde
Da sarkar da ido ba ya gani
Ca! ca!!
Su na tadina
Akwatunan surutu
Yadda ka san aku mara abun yi
Da ke yini guda ya na surutu
Ca! ca!!
Sai kirgawa su ke
Sa’ar da su ke wucewa kamar lilo
Mutane ma su neman na abinci
Don kuwa su nasu surutune
MA’ANA DA SHARHI
Wannan wake fassarar waken Turanci ce da na rubuta mai suna “The Idle Minds” wadda za ku iya samu a wannan shafin. Na rubuta wannan wake ne a lokacin da na ke zama a unguwa cikin mutane masu yawan sa ido kan harkar mutane, wanda kullum su na zaune kan benci su na yi da mutane masu wucewa.