WAKE: INA NI?

Ina ni?
Ina ni?
Mantawa da ke
A kayyadaddun ranakun da na ke da su
Wadanda ke kirguwa yini-yini
Kamar digon ruwan batur
Mai diguwa daga kwalba

Hannuwa a kugu ki ka tsaya
Tare da zuciyarki
Cike bam
Da kauna da kudurcewa
Domin ki ga na tsallake siratsan rayuwa
Kuma dukkan shingaye
Sun rikide zuwa taurari
Don haskakemin hanya
A yayin da na fito ga shahara

Ina ni?
Yin butulci a gareki
In zan manta da ke
Dai-dai da kwayar zarra
A zuciyata, jikina da ruhina


Tunaninki
Ruwana mai zafi
Da ke gudana daga zuciyata
Ga jijiyoyin jinina
Har zuwa ran da za a
Shimfide ni a kushewata

Duk wani mataki
Na shahara da daukaka
Da na kai
Kaddara ce tabbatarciya
Amma ke ce tsanin
Da ya tsaya cak
Da kafafuwanki
Ya na jure dukkan matsi
Don ganin na hau kololuwar sama


In ba dun sararin sama
Zai zame min iyaka ba
Ba za ki taba gajiyawa ba
Bisa ga kwazonki
Na gani na ina tashi
Cikin nasara
Zuwa ga kololuwa


Ina ni?
Ina kin yabawa da kwazonki?

MA’ANA DA SHARHI

Wannan fassarar wake cikin harshen Turanci ce da na rubuta ga mahaifiyata wadda za a iya samu a wannan shafin. Allah ya jikan iyayenmu da Rahama. Allah ya sa Aljannah ce makomarsu, Ameen Summa Ameen.


Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Hi, how can I help you?