Sa’ar Kiyama
Kamar yadda duniya ke juyawa cikin sauri
Hannayan agogo ke tafiya
Da kika bayan dakika
Minti bayan minti
Sa’a bayan sa’a
Zuwa ga sa’ar kiyama
A wannan sa’a minti da dakika
Ko wane rai
Zai girbe abun da ya shuka.
MA’ANA DA SHARHI
Wannan wake fassarar wake ta Turanci ce da na rubuta wadda a iya samu a wannan shafin. Wannan wake na magana akan sa’ar alkiyama da ta ke kusantarmu a kowacce sa’a.