NAJERIYA

NAJERIYA
Babbar kasata Najeriya
Uwa abar kaunata Najeriya
Ni danki bil adama
Na yi alkawarin sa ki alfahari
Na dawo da tsarki ga kasarki
Na zare takobina
Na fille kan mugu
Da burinsa ya ga kin kunyata


Babbar kasata Najeriya
Uwa abar kaunata Najeriya
Ni albarkar mahafarki
Nai alkawarin kareki
Na kunsheki
Cikin dimin garkuwata
Daga takuba da masun
Lalatattun ‘ya ‘yanki


Babbar kasata Najeriya
Uwa abar kaunata Najeriya
Nai alkawarin ni’imta ki
Da zufar aiyukana
Na ga kin fito gwarzuwa
A gasar sassan duniya
Na ma su shi da marasa shi.

MA’ANA DA SHARHI

Wannan wake fassarar wakar Turanci ce da na rubuta a wannan shafin. A wannan wake ina nuna kishi da kauna ga kasata Najeriya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Hi, how can I help you?