KUNYATA

Kunyata
Jikina na bari
Daga sanyin marmaro mai kamar zazzabi
Da kamar zai digo daga goshina
Kashin bayana kamar ya daskare
Zuciyata kuma baibaye da bakin ciki
Kafafuwana da aka ci da yaki
Sun tsaya cak
Su kai fatan kuma
Kasa ta hadiye su
Duniya da dubanta mai dafi
Ta kyalkyale da dariya
A sa’ar da na rarrafa ga ramina.

MA’ANA DA SHARHI

Shin wani abu ya taba faruwa da kai na kunya da ka ji kamar gwanda kasa ta hadiyeka? Wannan wake fassarar wake ce ta Turanci wadda za a iya samu a wannan shafin nawa.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Hi, how can I help you?