CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI

KANJAMAU
Su na kirana ‘Aids’
Yayin da ba na ba da wani agaji
Ina ni?
Ni uwar masifu


Ba zato ba tsamani sai karshe
Na ke kaiwa
Rayuwar kilaki
Kuma ba na kai gwiwa kasa
Don kawo rabuwa tsakanin
Ma’aurata masu yawo

Ina marayantar da tayi da ke mahaifa
Kafin ya iso
Ya tarar da hukuncin
Laifin da bai yi ba
Don kuwa babu alkalin
Da zai tserar da shi
Daga bala’in dafina


Kar ka damu da amfani da kwaroro
Don koyaushe da garkuwata na ke tafe
Na kawo maka kunci madawami
Bayan kololuwar dadin dakiku


Gurbatattun wukake da allurori
Gurbatattun wukaken fida da makana
Karin jinin da ba a duba ba
Da kuma ‘almakashin kowa’ na mai gyaran farce
Dalibai na ne
Da ba sa barin ko da tsarkakke
Ba a kadartoni dan horar da talaka ba
Sai don na hukunta kilaki
Na kuma ja mazinaci
Ga kushewarsa

Ina son matasa
Masu zinace-zinace
Don ba na kai kasa gwiwa
Don ganin sun sheka barzahu
Ina yaduwa kamar wutar daji
Don karar da jinsin bil adama
Don ni kadaice mai nasara a wannan tseran

A halin yanzu dai
Ba wani tsimin tukunya
Ba maganin asibiti
Kuma ba wani sihirinka mai sihiri
Da zai shammaceni
Ni da ku mutu ka raba

MA’ANA DA KUMA SHARHI

Wannan wake mai suna Kanjamau fassarar wake ce da nai da harshen Turanci mai suna iri daya wanda za a iya samu a wannan shafin. Na kwaikwayi salon rubutun wake ta Turanci mai suna ‘Abiku’ da Wole Soyinka ya yi.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Hi, how can I help you?